<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Yesu Ɗan Allah ne, Mai Ceton duniya,
 Ya ƙaunace mu har ga mutuwa.
 Wanda ya ba da gaskiya gare shi
 Lalle ya tsira daga shari'a.

[V2]
 KORUS
 Yesu mai iko duka ne,
 Ba za ya kasa ba daɗai,
 Sai mu kai bishara ko'ina a duniya
 Shi kuwa za ya taimake mu.

[V3]
 2) Ƴanuwanmu sun ƃata cikin duhu,
 Ba su da rai, ko sanin hanyarsa.
 Kada su mutu cikin zunubansu,
 Sai dai su zo su sami gafara.
 Korus

[V4]
 3) Ubangijinmu za ya sake zuwa
 Domin ya kai mu can a gidansa.
 Me za mu ce idan mun ƙi biyayya?
 Me za mu amsa masa ranan nan?
 Korus

[V5]
 4) Sauri, jama'a, Yesu yana kiran
 Duk Masu Bi su kama aikinsa.
 Maza da mata duk da yara kuma,
 Tashi, mu yi biyayya nandanan.
 Korus</lyrics>
<title>Yesu Ɗan Allah Ne, Mai Ceton Duniya LW270</title>
<hymn_number>270</hymn_number>
</song>